Dakarun Iraqi sun kwace garin Nimrud daga mayakan IS

IS

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

IS ta ce ba za ta bari a rika bautawa gumaka ba

Dakarun sojin Iraqi sun ce sun kwace birnin nan mai dimbin tarihi na Nimrud, wanda ke hannun mayakan IS shekara biyu da suka wuce.

A watan Maris na shekarar 2015, jami'ai da masana tarihi sun yi tur da IS saboda rushe birnin, wanda aka gina tun karni na 13, da ta yi.

Hukumar kula da tarihi ta majalisar dinkin duniya ta bayana rusa birnin da cewa laifin yaki ne.

Kungiyar IS dai ta ce zuwa hubbare da kuma gina mutum-mutumi bautar gunki ce, wadda ya kamata a hana.

Birnin na Nimrud yana da nisan kilomita 30 daga birnin Mosul, wanda dakarun sojin na Iraqi suka kaddamar da hare-hare domin sake kwace shi tun a watan jiya.

Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta ce : "Dakarun runduna ta Tara sun kwato Nimrud bakin daya kuma sun kafa tutar Iraqi a birnin bayan sun karkashe mayakan IS."