Ghana: An kai hari gidan jagoran 'yan adawa Akufo Addo

'Yansandan Ghana
Bayanan hoto,

Mr. Addo dai baya a gidan lokacin wannan arangamar.

A kasar Ghana, masu gadi da 'yansanda sun tarwatsa wani gungun jama'a da suka kai wa gidan jagoran 'yan adawa na kasar hari ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce mutanen sun rika jefa kwalabe da duwatsu gidan Nana Akufo Addo lamarin da ya sa har sai da 'yansanda suka rika harbin iska domin tarwatsa su.

An yi zargin cewa masu harin, magoya bayan jamiyyar da ke mulkin kasar ne wadanda ke cikin masu wani tattaki na motsa jiki da suka biyo ta kofar gidan shugaban 'yan hamayyar wanda ke takarar shugabancin kasar a inuwar jam'iyyar NPP.

Amma jam'iyyar mai mulki ta NDC ta musanta cewa magoya bayan nata ne suka fara kai hari kan gidan; inda ta ce sun mayar da martani ne kan harbin gargadi da masu gadin gidan suka yi lokacin da jerin gwanon masu tattakin ke wucewa kusa da gidan.