Zaben Trump: An bai wa Priebus da Bannon manyan mukamai

Shugaban Kwamitin zartarwar na jam'iyyar Refablika Reince Priebus

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana ganin Reince Priebus a zaman tsani tsakanin Donald Trump da masu adawa da shi a jam'iyyarsu.

Shugaban kasar Amurka mai-jiran-gado Donald Trump ya bayar da manyan mukamai ga wani kusa a jam'iyyar Refublika da kuma shugaban wata kafar watsa labarai.

Reince Priebus, Shugaban Kwamitin zartarwar na jam'iyyar Refublika, zai kasance shugaban ma'aikata a fadar White House.

Stephen Bannon kuwa, wanda tsohon shugaban gidan tallabijin na Breitbart News Network ne, zai yi aiki a zaman babban mai tsara dabarun mulki ga Mr. Trump.

Mr. Bannon ya sauka daga mukaminsa na shugaban kafar watsa labaran ta Breitbart na wucingadi domin ya shugabanci yakin neman zaben Donald Trump.