Nigeria: 'Yan sanda sun yi arangama da 'yan Shi'a a Kano

Asalin hoton, IMN
Hotunan da 'yan Shi'a, da ke goyon bayan Sheikh El-zakzaky, suka afitar sun nuna 'yan sanda suna rufe hanya
Akalla mutane takwas aka kashe lokacin da 'yan sanda suka yi arangama da 'yan Shi'a a wajen birnin Kano na Nigeria, yayin da aka kashe wani dan sanda daya.
Jami'an tsaro sun ce daya daga cikin 'yan sandan na nan rai a hannun Allah.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wani mutum yana cewa ya ga gawarwakin mutum goma.
Wani dan jarida da ke tafiya da 'yan Shi'ar ya shaida wa BBC cewa 'yan sanda sun harbi mabiyansu da dama, kuma akwai fargabar an kashe mutane da yawa.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim cewa ya ga motocin 'yan sanda dauke da mutane hudu da harin ya shafa, amma ba tabbas ko sun mutu ko suna raye ba.
Kungiyar ta 'yan Uwa Musulmi, wacce ke goyon bayan kasar Iran, na da tarihin yin fito-na-fito da jami'an tsaron Nigeria.
Akalla magoya bayanta 349 aka kashe a watan Disamban bara lokacin wata arangama da suka yi da sojoji a garin Zaria.
Asalin hoton, IHRC
Mabiya Shi'a a Najeriya sun dade suna fito-na-fito da jami'an tsaro
'Yan sanda sun tabbatar da rikicin na baya-bayan nan, amma kakakinsu a jihar Kano Magaji Majiya ya ce har yanzu suna tattar bayanai.
Sai dai wani jami'i da bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce sun bude wuta ne saboda 'yan Shi'ar sun kai musu hari.
Ya kuma kara da cewa ana ci gaba da bata-kashin.
Yanzu haka an toshe babbar hanyar shiga garin Kano daga kudu, da kuma fita zuwa babban birnin kasar Abuja saboda rikicin.
Mabiya Shi'ar na yin tattakin da suka saba yi ne a duk shekara zuwa garin Zaria, mai nisan kilomita 165, inda nan ne cibiyar kungiyar ta su.