IS ta kai munanan hare-hare a birnin Bagadaza

Iraqi Karbala
Bayanan hoto,

Kungiyar IS ta sha kai hare-hare a kasar Iraqi

Fararen hula takwas ne aka hallaka, yayin da wasu karin biyar suka samu raunuka a wani harin kunar-bakin-wake a kudu maso yammacin birnin Bagadaza na kasar Iraqi.

'Yan harin kunar-bakin-waken sun shiga garin Ain Tamr, daga yammacin lardin Anbar da sanyin safiyar Litinin, amma sun gamu da turjiya daga jami'an tsaro.

An bindige biyar daga cikin maharan, amma shida sun kutsa cikin wani gida inda suka tarwatsa kansu tare da hallaka fararen hula.

Kungiyar da ke kiran kanta Kasar Musulunci wato, IS ta ce ita ke da alhakin kai harin.

A ranar Lahadi ta kaddamar da jerin hare-haren bama-bamai a ciki da wajen birnin Bagadaza, abin da ya hallaka akalla mutane 23, tare da jikkata wasu 70.

Mahukunta sun ce 'yan harin kunar-bakin-waken da suka kai hari a garin na Ain Tamr, sun sha yunkurin kutsawa birnin Karbala, inda 'yan Shi'a ke da rinjaye, mai tazarar kilomita 50 daga gabashin kasar.

Miliyoyin 'yan Shi'a ne ke yin tattaki zuwa birnin Karbala don yin bikin kawo karshen makokin kwanaki 40 na Limamin Shi'a na uku Hussein.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Miliyoyin 'yan Shi'a na yin tattaki zuwa Karbala a Iraqi

Za a gudanar da bikin na wannan shekarar a ranar Lahadi.

Hussein, jikan Annabi Muhammad ( SAW) ne, kuma an hallaka shi a yakin Karbala ne, a cikin karni na bakwai, a ranar da ake kira Ashura.

Sai dai 'yan Sunni masu tsattsauran ra'ayi na daukar 'yan Shi'a a matsayin masu sabo, da hukuncin kisa ya hau kansu, saboda a cewarsu suna amfani da sunayen iyalan manzon Allah wajen saba wa dokokin addinin Musuluci.

Kungiyar IS ta sha kai hare-hare a kasar Iraqi tun bayan da dakarun gwamnati suka kai wani babban farmakin kwato birnin Mosul da ke arewacin kasar, daga hannun mayakan.