Firai Ministan Jamhuriyar Dumukuradiyyar Congo ya yi murabus

Augustin Matata Ponyo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Augustin Matata Ponyo, ya yi murabus karkashin yarjejeniyar zaman lafiya

Firai Ministan Jamhuriyar Dumukuradiyar Congo, Augustin Matata Ponyo, ya yi murabus domin bayar da dama ga wani daga cikin jiga-jigan 'yan hamayya.

Hakan dai na daga cikin wata yarjejeniyar da aka cimma a tattaunawar watan da ya wuce da ke nufin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Karkashin yarjejeniyar ana sa ran jinkirta zaben da aka yi niyyar gudanarwa a cikin watan Disamba har sai zuwa shekara ta 2018.

Manyan jam'iyyun hamayya dai sun kaurace wa zaman tattaunawar, suna zargin Shugaba Joseph Kabila da yunkurin cigaba da mulki.

Mutane da dama ne aka hallaka yayin zanga-zangar nuna adawa da dage zaben.