Pakistan ta ce india ta kashe sojojinta 7

Pakistan India

Asalin hoton, ISPR

Bayanan hoto,

Babban hafsan sojin Pakistan Raheel Sharif ya jagoranci jana'izar sojojinsu 7 da suka mutu

Rundunar sojin Pakistan ta ce sojojinta bakwai sun mutu a wani luguden wuta da dakarun India suka yi a yankin Kashmir da kasashen ke takaddama a kansa.

Babban hafsan sojin kasar Pakistan din Raheel Sharif da sauran jami'ai sun gudanar da sallar jana'izar sojojinta da aka hallaka a wata musayar wuta a kan iyaka

Wasu rahotanni sun ce wannan ita ce asarar rayuka mafi muni a yankin na Kashmir da Pakistan din ta yi a lokaci guda tun bayan yarjejeniyar shekara ta 2003.

Kasashen India da Pakistan na zargin junansu da karya yarjejeniyar tsagaita wutar ta shekara ta 2003.

Tashin hankalin ya ta'azzara kan dadadden rikicin tun bayan kai wani hari kan sansanin sojin India a cikin watan Satumba.

Duka bangarorin sun ba da rahoton kashe musu fararen hula da dama, ko kuma jikkata a makonnin baya, lokacin da aka yi ta ba-ta-kashi a yankin.

Daruruwan fararen hula ne a kauyukan da ke kusa da yankin da ake takaddamar a kai aka kwashe, domin kare su.