Zaben Trump ya jawo samun karuwar tallafin zubar da ciki

Asalin hoton, Reuters
Mataimakin Donald Trump, Mike Pence na adawa da zubar da ciki
An samu karuwar bayar da taimako ga daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke taimakawa wurin zubar da ciki, Planned Parenthood, sakamakon zaben Donald Trump da mataimakinsa.
Ana aika tallafin ne da sunan mataimakin Trump din Mike Pence wanda yake matukar adawa da zubar da ciki, a matsayin wani shagube domin kunyata shi.
Za a aika wa Mista Pence takardar shedar duk taimakon da aka bayar ga kungiyar ta Planned Parenthood, da sunansa.
A lokacin da yake dan majalisar wakilan Amurka na Indiana, kuma daga bisani ya zama gwamnan jihar, Mista Pence ya bullo da tsauraran matakan hana zubar da ciki a Amurka.