A Kenya wasu iyaye sun raɗa wa ɗansu suna Donald Trump

Donald Trump

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Iyayen jaririn sun ce Donald Trump yana burge su

Wasu iyaye sun bayyana dalilin da ya sa suka sanya wa jaririnsu sunan sabon zababben Shugaban Amurka Donald Trump, bayan da ake ta sukansu kan yin hakan.

An haifi jaririn wanda cikakken sunansa shi ne Donald Trump Otieno, ranar tara ga watan Agusta a yankin Kisumu na yammacin ƙasar.

Kuma iyayen nasa sun yanke shawarar raɗa masa wannan suna ne mai jawo ce-ce-ku-ce, saboda sun yaba da aƙida da manufar Mista Trump, kamar yadda jaridar Daily Nation ta Kenyan ta ruwaito.

Mahaifin jaririn mai suna Felix Otieno, ya ce sun sanya wa ɗan nasu sunan ne tun kafin hamshakin ɗan kasuwar ya kayar da Hillary Clinton a zaɓen shugaban Amurkan.

Mista Otieno ya bayyana cewa, '' a lokacin ba ni da tabbacin Trump zai bayar da mamakin da ya bayar na nasarar da ya yi, amma dai ina da yaƙinin cewa yana da cancanta ta zama shugaba.''