Nigeria za ta sayar da wasu matatun manta

Matatar mai a Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gwamnati za ta bai wa matatun man damar farfadowa daga halin da suke ciki

Wani daftarin manufofin gwamnatin Najeriya a fannin harkar mai da gas ya nuna cewa kasar na shirin sayar da matatun manta da ba sa samar da riba kamar yadda ya kamata.

Daftarin ya bayyana cewa za a bai wa kowacce matata tallafin da ya dace domin ganin ko za ta farfado kafin a dauki matakin sayarwar.

Najeriya tana da matatun mai guda hudu ne kawai kuma tana shigo da akasarin albarkatun man fetur dinta ne, duk da cewa tana samar da gangar mai miliyan biyu a kullun.

Matatun man kasar dai sun kasance ba sa aiki a mafiya yawan lokuta.

Gwamantin Najeriya ta dauki wannan mataki ne a wani bangare na wani muhimmin shirinta na yin garanbawul a masana'antun man.

Za kuma a samar da hukumar saka ido kan albarkatun man wacce za a kira Petroleum Regulatory Commission.

Daftarin ya nuna cewa ba a amfani da ka'idojin da ya kamata a bi wajen tafiyar da harkokin man fetur a kasar.