Labaran karya na karuwa a shafin Facebook

Mark Zukerberg Facebook

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An kara kaimin bincike kan yadda labaran karya ke karuwa a Facebook

Duk da kokarin da Mark zuckerberg ya yi domin rage muhimmancin zaben Donald Trump a Facebook, an kara matsa kaimi kan yadda labaran karya ke karuwa.

Shafin Buzzfeed ya bada rahoton cewa ma'aikatan kamfanin Facebook ''fiye da dama" na wani yunkuri na kashin kansu don shawo kan matalar.

Buzzfeed din ya ambato kalaman daya daga cikin wadannan ma'aikata wanda ba ya so a ambaci sunansa saboda tsoron rasa aikinsa, ida yake cewa:

"Mark Zukerberg'' ya sani, kuma wasunmu a kamfanin sun sani, cewa labaran karya na yaduwa kamar wutar daji a shafukanmu lokacin da guguwar yakin neman zaben ke kadawa'.'

Kamfanin na Facebook bai maida martani kan rahoton na Buzzfeed ba, kamar yadda BBC ta nema.

A ranar Litinin ne Facebook ya musanta ikirarin cewa an kirkiri wani abu da zai rage yada labaran karya kafin zaben, amma kuma hakan ya gamu da cikas saboda kada a yi zargin cewa Facebook din na bincike kan bayanan masu ra'ayin rikau.

Mr Zuckerberg ya kara harzuka kan bayanan da suka nuna cewa gurbatattun labarai babbar matsala ce a shafinsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mr Zuckerberg ya harzuka kan batun karuwar labaran karya a Facebook

A daren ranar Asabar ne ya wallafa dogayen bayani a shafinsa na Facebook yana kare batun.

"A duka bayanan da ke kan shafin Facebook, fiye da kashi 99% na abin da mutane ke gani sahihai ne,'' a cewarsa.

A cikin watan Mayu ne Facebook ya fuskanci suka, bayan da aka zarge shi da amfani da wasu editoci dake aiki kan labarai mafiya shahara, inda suke cire labaran magoya bayan Trump ko na masu ra'ayin rikau.

Facebook dai ya musanta hakan, amma kuma ya cire wasu abubuwan a wani yunkurin nuna cewa ba shi da hannu.