Russia: An cafke ministan tattalin arziki kan cin hanci

Mr Ulyukayev Russia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mr Ulyukayev shi ne minista na farko a kasar Russia da aka taba cafkewa a lokacin shugaba Putin

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Russia SK ta cafke ministan harkokin tattalin arziki na kasar Alexei Ulyukayev.

Hukumar ta SK ta ce ministan ya karbi cin hancin dala miliyan biyu.

Mr Ulyukayev shi ne mai rike da mukami mafi girma a kasar ta Rasha da aka taba cafkewa tun bayan yunkurin juyin mulki a shekara ta 1991.

Hukumar ta ce ya yi ''barazanar'' hana ruwa gudu ga ayyukan kamfanin mai na kasar Rosneft lokacin da ya karbi kashi 50 bisa dari na ayyuka a daya kamfanin mai na kasar Bashneft.

Kakakin hukumar ta SK Svetlana Petrenko, ta ce "an kama Ulyukayev da hannu dumu-dumu'', yana karbar dala mliyan biyu a ranar 14 ga watan Nuwamba don ya amince da bukatun kamfanin na Rosneft.

Cafke Mr Ulyukayev ya zama wani babban labari a gidan talabijin na kasar ta Russia, da aka yiwa take ''Yaki ta cin hanci da rashawa''.

Idan dai aka same shi da aikata laifin zai fuskanci zaman gidan yari na shekara takwas zuwa 15.

A shekara ta 2004 ya zama shugaban babban bankin kasar ta Rasha.