Masar: Kotu ta soke hukuncin kisa kan Mohammed Morsi

Morsi Masar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Morsi na fuskantar daurin rai-da-rai kan aikata laifin ta'addanci

Wata babbar kotun kasar Masar ta soke hukuncin kisan da aka yanke wa hambararren Shugaban kasar Mohammed Morsi.

An yankewa Morsi hukuncin kisan ne saboda samun shi da hannu a fasa gidan yari lokacin juyin juya halin 2011 a kasar.

A shekara ta 2012 ne aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, amma sojoji suka tunbuke shi bayan shekara guda lokacin da aka yi wata zanga-zangar nuna kin jinin mulkinsa.

An yanke wa Morsi hukuncin daurin rai-da-rai daban kan aikata laifukan ta'addanci, kana yana fuskantar shari'a kan wasu tuhume-tuhume.

Hukuncin na ranar Talata da kotun Cassation ta yanke na nufin za a sake yi wa Morsi shari'a kan fasa gidan yarin.

Kotun ta kuma soke hukuncin kisa kan shugabanni biyar na kungiyar "Yan Uwa Musulmi da aka haramta, da suka hada da jagoranta Mohammed Badie.