Za a yi garambawul a harkar sufurin jiragen saman Nigeria

Ma`aikatar sufurin jiragen sama ta Nigeria ta ce za ta yi garambawul ga harkar sufurin jiragen saman kasar don tafiya da zamani da habaka kudin-shiga.

Gyaran-fuskar zai hada da tankade da rairayar ma`aikatan da ke hukumomin sufurin jiragen sama, da inganta filayen saukar jirage ta yadda manyan jiragen za su iya sauka a kasar.

Ministan harkokin sufurin jiragen sama na Nigeria, Senata Hadi Sirika, ya shaida wa BBC cewa akwai abubuwan da ba sa tafiya daidai a fannin.

Ga karin bayanin da ya yi wa Ibrahim Isa a Abuja: