Buhari: Ibrahim Dasuki jigo ne na zaman lafiya

Shugaba Muhammadu Buhari
Bayanan hoto,

Buhari ya ce marigayi Sultan Ibrahim Dasuki, ya yi aiki tukuru wajen hada kan 'yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Sarkin Musulmi na 18 Alhaji Ibrahim Dasuki amatsayin jigo wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.

Shugaban ya aike da sakon ta'aziyyar Sultan din na 18 ne wanda ya rasu ranar Litinin yana da shekara 93, ga iyalansa da gwamnati da kuma al'ummar jihar Sokoto, ta hannun babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu.

Shugaba Buhari, ya kuma jajanta wa kungiyar Jama'atul Nasril Islam da Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, kan rashin tsohon Sarkin Musulmin, wanda ya ce ya yi rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta juna tsakanin al'ummar kasar daban-daban.

Ya kuma yaba wa marigayin wanda ya ce ya yi rayuwa irin ta Sardauna wanda ya yi aiki da shi, kan gudummawar da ya bayar ta zamanantar da tsarin sarautar gargajiya.

Sannan ya ce za a dade ana tuna marigayin kan rawar da ya taka wajen samar da rahoton da ya kai ga kirkiro tsarin kananan hukumomi da ake aiki da shi yanzu a Najeriya.