Boko Haram ta sake kashe wani hafsan sojin Najeriya

Sojojin Najeriya
Bayanan hoto,

An kashe kwamandan ne lokacin da yake duba illar da nakiya ta yi wa motarsu

Mayakan Boko Haram sun sake kashe wani kwamandan sojin Najeriya, Laftana Kanar B.U. Umar, a wani harin kwantan bauna a jihar Borno, ranar Litinin.

Jaridar Premium Times wadda ke watsa labaranta ta intanet, wadda ta bayyana labarin ta ce wata majiya ce ta sojin Najeriyar ta shaida mata labarin.

Jaridar ta ce, mayakan sun bude wa hafsan sojin wanda shi ne kwamandan bataliya ta 114 (114 TF Battalion) ta sojin kasa na Najeriya, a lokacin da ya sakko daga motarsu da ta taka nakiya, yake duba wa illar da motar ta yi, amma a lokacin shi bai ji rauni ba.

Rahoton ya ce hafsan da dakarunsa suna kan hanyarsu ne ta zuwa Yola babban birnin jihar Adamawa, daga Bita da ke jihar Borno a lokacin da aka yi musu kwantan-baunar, tsakanin Bitan da Pridang.

Kawo yanzu ba a san yawan wadanda suka hallaka a harin ba, kuma kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman ya ce ba shi da labarin mutuwar kwamandan a lokacin da jaridar ta tuntube shi.

B.U. Umar wanda ya karbi shugabancin bataliyar kimanin makonni uku da suka wuce, yana daga cikin daliban makarantar kananan hafsoshin sojin Najeriya ( NDA) 'yan cikakken kwas na 48.

Kusan mako daya kenan da 'yan Boko Haram din suka kashe wani hafsan na sojin Najeriya, Laftana Kanar Muhammed Abu-Ali, da dakarunsa a wani harin kwantan-bauna.