BBC za ta bude sabbin sassan harsuna 11

Ginin BBC
Bayanan hoto,

Ana dai sa ran sabbin sassan da za a bude su fara aiki a shekara mai kamawa.

BBC ta kaddamar da wani shirin fadada aikace-aikacenta a sashenta mai watsa shirye-shirye zuwa kasashen waje mafi girma tun shekarun 1940.

Manufar wannan matakin dai ita ce kai labarai na gaskiya da babu son rai a ciki ga karin miliyoyin mutane a sassa daban-daban na duniya ciki har da kasashen da 'yancin kafafen watsa labarai ke fuskantar barazana.

Haka ma sashen na BBC World Service zai fadada kafofinsa na isar da sakonni ga masu kallo da saurarensa ta shafukkan internet da na sada zumunta.

Bayanan hoto,

BBC ta shafe shekara da shekaru tana taka rawa

Sashen dai zai bude wasu sabbin sassa da zu rika watsa shirye-shirye a cikin harsuna 11; abin da zai kai adadin harsunan da yake watsa shirye-shiryensa a ciki zuwa 40.

Sabbin harsunan sune na Afaan Oromo, da Amharic, da Gujarati, da Igbo, da Koriyanci, da Marathi, Turancin fijin, Punjabi, Telugu, Tigrinya, da kuma Yarubanci.