Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa

Donald Trump da tawagarsa

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

Donald Trump ya kare rade radi da ake cewa akwai matsala a tawagarsa

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya kare shirinsa na karbar mulki yayinda ake tsaka da samun rashin jituwa a cikin tawagarsa.

Mista Trump, hamshakin mai hada-hadar gidaje ne kuma sabon shiga ne a jam'yyar Republican wanda ya yi nasarar ba-zata a kan Hillary Clinton.

Tuni dai Trump ya maye gurbin gwamnan New Jersey Chris Christies da zababben mataimaki Mike Pence a matsayin shugaban kwamitin mika mulki.

Kafafen yada labarai na Amurka sun ce an tursasa wa manyan mambobin kwamitin mika mulkin biyu, wandanda ke aiki kan tsaron barin ayyukansu.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce surikin shi da kuma Jared Kushner wani mai ba shi shawara wanda yake da kusanci da shi suna da hannu a sauyin.