Mata ta kai ƙara kan ganin mushen ɓera a sabuwar rigarta

Asalin hoton, Facebook
Cailey Fiesel, ta ce doyin da ta rika ji ne a jikinta ya sa ta gano mushen beran
Wata mata a birnin New York na Amurka, ta gano wani mataccen bera da aka dinke a cikin wata sabuwar riga da ta saya.
Matar mai suna Cailey Fiesel ta ce ta sayo wata riga ta dala 40 a kamfanin sayar da tufafi, Zara, amma kuma bayan 'yan makonni tana zaune a wurin aikinta sai ta rika jin wani doyi a jikinta.
Ms Fiesel, mai shekara 24, ta ce ta ji dan wani abu ya karce ta a kafa, da ta duba sai ta ga kafar bera ta dan leko daga lafin rigar tata.
Ta ce, '' sai kawai na kame, na suma a tsaye, ban san ta yi ba, ina cike da tsoro,'' kamar yadda ta sheda wa jaridar New York Post.
Asalin hoton, Facebook
Ba a bayyana yawan kudin da take neman kantin tufafin, Zara, da ta sayi rigar ya biya ta ba.
Matar dai ta shigar da kara a kan kantin na sayar da tufafi mai cibiya a Spaniya, Zara.
Lauyoyin Ms Fiesel sun yi zargin cewa matar ta yi fama da matsalar damuwa sannan kuma wasu kuraje sun fito mata, wadanda likitoci suka danganta da bera.
Kakakin kantin na Zara, reshen Amurka ya ce, kamfanin yana sane da karar kuma suna gudanar da bincike a kai.
Ya ce, Zara USA, yana da tsauraran dokoki da tsare-tsare na tabbatar da ganin kayansa sun kiyaye da ka'idoji.