Giyar gargajiya ta kashe mutum 21 a Kamaru

Hukumomin Kamarun sun hana yin barasar sakamakon lamarin, kuma yawancin wadanda abin ya shafa mata ne.
Wasu mutane 21 sun mutu a Kamaru bayan da suka sha wata giyar gargajiya mai karfin tsiya, a wani yanki na kasar Kamaru.
An kuma garzaya da wasu mutanen 22 da su ma suka kwankwadi barasar wadda ake kira Odontol, kamar yadda kafafen watsa labarai na gwamnatin Kamarun suka sanar.
A yanzu dai hukumomi a garin Abong-Bang, na Kudancin Kamaru, inda lamarin ya faru, sun haramta yin giyar.
Ana yin giyar ne da ruwan bishiyar kwakwa, wato bammi da sukari da kuma bawon wata bishiya da ake kira essok a yankin.