An yi Shari'ar farko ta 'yan luwadi a Ivory Coast

Homosexual act
Bayanan hoto,

Luwadi ba haram ba ne a Ivory Coast amma yin dabi'ar 'yan luwadi a fili laifi ne

Hukumomin Ivory Coast sun yi shari'ar farko ta 'yan luwadi biyu a kasar, inda aka yanke musu zaman gidan sarka na watanni goma sha takwas.

Kafafen watsa labarai na kasar ba su bayyana sunayen mutanen biyu ba, inda aka yi musu inkiya da, P.L., mai shekara 31 da kuma L.A., mai shekara 19, wadanda suka fito daga wani kauye a kudu-maso-yammacin kasar.

Kawun karamin daga cikinsu ne ya gan su lokacin da suke saduwar, kuma nan da nan ya kai rahotonsu gun 'yan sanda.

Mutanen biyu sun amince cewa suna soyayya ta luwadi a junansu, amma kuma sun ce, su ba su san cewa hakan laifi ne ba, kamar yadda rahoton jaridar intanet ta Abidjan.net ta bayyana.

Ba a haramta luwadi a kasar ta Ivory Coast ba, amma laifi ne a yi wani abu da ya shafi luwadi a bayyanar jama'a.