Zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger

Rakuma

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Zazzabin Rift Valley hasali cutar dabbobi ce kamar awaki, akuyoyi da kuma rakuma.

Akalla mutum 32 sun mutu tun watan Agusta sakamakon zazzabin Rift Valley a Niger kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito ma'aikatar lafiyar kasar na cewa.

A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta fitar, ta ce annobar ta bazu a yankin Tahoua, inda mutum 230 suka kamu da ita.

Zazzabin Rift Valley dai cuta ce da sauro ke yadawa - hasali ma dai cutar dabbobi ce kamar awaki, akuyoyi da kuma rakuma.

Sai dai makiyaya da masu kula da dabobbi suna da hadarin kamuwa da cutar kamar saboda zai iya yaduwa ta hanyar taba jinin dabba ko kuma idan sauron da ya kuma da cutar ya cije mutum.

Alamomin cutar na farko da ke bayyana a jikin mutum sun hada da zazzabi da ciwon kai wanda zai iya tsananta zuwa fitar da jini daga dadashi da hanci a wasu lokutan ma mutum ya shiga halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce yawan mace macen da ake yi ya ragu da kashi 50 cikin 100 a cikin watanni uku da suka wuce zuwa kashi 14 cikin 100, sakamakon wani shirin wayar da kan jama'a na gwamanti, da ya bukaci mutane su rika birne gawarwakin dabbobi tare da yin takatsantsan wurin mu'amala da matattun dabbobi da kuma gujewa shan madara wadda ba a gauraya ba.