Fiye da mutane 70 sun hallaka a Mozambique

Lamarin dai ya faru ne a lardin Tete dake kusa kan iyakar kasar da Malawi
Hukumomi a kasar Mozambique sun ce fiye da mutane 70 ne suka mutu yayin da 110 suka samu munanan raunuka bayan da wata babbar motar dakon man fetur ta fashe ta kuma kama da wuta.
Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce mutanen da lamarin ya rutsa da su suna kokarin kwasar man fetur ne bayan da babbar motar dauke da man fetur ta fadi ta kama da wuta saboda tsananin zafi.
Lamarin dai ya faru ne a lardin Tete dake kusa kan iyakar kasar da Malawi.
Tuni gwamnati ta turo jami'ai zuwa yankin domin tantance lamarin da kuma irin taimakon da mutanen ke bukata.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya da BBC Safe 23/01/2021, Tsawon lokaci 1,13
Minti Ɗaya Da BBC na Safiyar 23/01/2021, wanda Nabeela Mukhtar Uba da Sani Aliyu su ka karanto.