Mai gyaran takalmin da 'ya fi masu albashi samun kudi'

  • Usman Minjibir
  • BBC Hausa
Yana gyaran takalma har ma da tankin ruwa na roba
Bayanan hoto,

Idris yana bi kwararo-kwararo domin neman kwastomomi

Idris, mai shekara 21, na daya daga cikin dimbin matasa masu sana'ar gyara da wanke takalma, a Najeriya.

Idris wanda dan asalin garin Isa ne da ke jihar Sokoto, yana bi kwararo-kwararo a garin Kuje da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja, domin neman aikin takalmi.

Ya kan fito bakin fama da zarar ya karya kumallo kuma ba ya komawa makwancinsa har sai la'asar sakaliya.

Mafi yawancin lokuta ma, Idris yana komawa gida ne gefin almuru.

Dauke da akwatu tare da akwakun da ke kunshe da kayan aikinsa, matashin yana karkada alharga tare da marikin akwatun wadanda haduwarsu ke bayar da sauti mai jan hankali ga kwastomominsa da ke cikin gidaje har ma da na waje.

Bayanan hoto,

Idris yana wanke takalmi a kan kudi Naira 50 ko 30

Idris ya fada min cewa duk da cewa mutane suna ta faman tsitsitsi da kukan rashin kudi sakamakon halin karayar tattalin arzikin da Najeriya ta samu kanta a ciki, har yanzu, ludayin masu sana'a irin tasa, na kan dawo.

"A kullum ta Allah na kan yi aikin Naira 3000, idan kuma ranar ba ta yi kyau ba, na kan iya komawa gida da N1500." In ji Idris.

Ya kuma kara shaida min cewa yana zuba adashin Naira Dubu a kowane wayewar garin Allah.

Sannan kuma ya ci abinci da biyan bukatun yau da kullum da ragowar kudin har ma ya taimakawa mahaifansa.

"Da wannan sana'ar nake taimakawa iyayena da 'yan uwana."

Bayanan hoto,

Idris yana wanke takalmi kafin ya shafa masa mai

Da na tambayi matashin ko ya yi karatun Boko domin samun shaidar da za ta ba shi damar yin aikin gwamnati domin samun albashi mai tsoka, sai ya kada baki y ace min "ban yi karatun boko ba kuma ba na yin da-na-sani."

"Sannan kuma ai nafi wasu ma'aikatan samun kudi a karshen wata tunda an ce wasu albashinsu bai wuce Naira dubu 39 ba."

To shin ko a nawa Idris yake wanke da gyara takalma?

"Idan na sanya wa takalmi neuteral, Naira 50 ne, idan kuma wanda ba neuteral ba ne, ina karbar Naira 30."

Baya ga wanke da goge takalmi, sana'a irin ta su Idris ta kunshi dinke takalman da sanya musu gam idan sun daga.

Har wa yau, Idris yana dinke jakunkuna har ma da gyaran tankunan ruwa na roba idan suna zubar da ruwan.

Bayanan hoto,

Shekarar Idris 21 da haihuwa

Dangane kuma da burinsa a rayuwa, na tambayi Idris, abin da yake son ya zama.

" Babban burina shi ne na zama mai kamfanin yin takalma da kowa zai san da zamana."

To babu dai abin da zai gagari ubangiji, amma a yanzu dai Idris na daya daga cikin daruruwan masu gyaran takalmi a kasar da ake yi wa kallon sana'arsu ba ta kai ga cire su daga marasa aikin yi ba.

Ko Idris zai mallaki katafaren kamfanin yin takalmin da yake mafarki, a nan gaba? Allah ne kadai masani. To amma dai da alama ya fi wasu masu daukar albashin da suke yi wa masu sana'a irin tasa kallon sai-da-kaji sai-da-kaji.

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin kayan aikin Idris ke nan a cikin kwando

Bayanan hoto,

Burin Idris dai shi ne ya mallaki kamfanin yin takalma