An sace mutum fiye da 40 a Zamfara

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sace-sace sun zama ruwan dare a Najeriya

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Nigeria sun ce 'yan bindiga masu fashin shanu sun sace mutane fiye da arba'in a jihar.

A ranar Juma'a ne da dai masu fashin shanun suka sace mutanen a lokaci guda domin yin garkuwa da su.

Akasarin mutanen da suka yi awon gaba dasu dai 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa daga kauyukansu.

Rahotannin sun kara cewa 'yansanda biyu da fararen hulla hudu sun rasa rayukansu a cikin lamarin.