Lee Cattermole zai yi jinyar watanni hudu

Lee Cattermole na Sunderland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lee Cattermole yaje Amurka domin a yi masa tiyata

Kungiyar Sunderland ta sanar da cewar, dan wasanta Lee Cattermole, zai yi jinyar watanni hudu sakamakon raunin da ya yi a kugunsa.

Catermole mai shekara 28, ya yi wa Sunderland wasanni biyu a gasar cin kofin Premier a bana, kuma tuni ya isa Amurka domin likitoci su yi masa tiyata.

Dan kwallon ya buga wa Sunderland wasansa na karshe a karawar da Crystal Palace ta doke su da ci 3-2 a gasar Premier da suka yi a ranar 24 ga watan satumba.

Kociyan Sunderland, David Moyes, ya ce 'yan wasa da suka hada da Jan Kirchof da Jack Rodwell da Fabio Borini ba za su buga fafatawar da za su yi da Hull City a ranar Asabar ba.