Za a yi wa fadar Buckingham kwaskwarima da £369m

fadar Sarauniyar Ingila

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Akasarin kayayyakin dake cikin fadar Sarauniyar Ingila an sanya ne tun a shekarun 1950

Za a kashe fam miliyan 369 wajen yiwa fadar sarauniyar Ingila kwaskwarima cikin shekara 10.

Ana saran amfani da harajin da al'ummar Burtaniya ke biya ne wajen aikin gyara fadar ta Buckingham.

Ayyukan da za'a yi sun hada da sauya hanyoyin wutar lantarki da ruwan famfo da kuma na'urorin dumama gida.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Za'a sauya hanyoyin wutar lantarki da ruwan famfo

Sai dai sarauniyar ba za ta fita daga cikin fadar ba a lokacin da za'a fara ayyukan a watan Afrilun shekara mai zuwa.

Jami'ai sun ce bayan an kammala kwaskwarimar fadar zata kasance na zamani tare da rage barnata makamashi.

Akasarin kayayyakin da suke cikin fadar ta Sarauniyar Ingila an sanya su ne tun a shekarun 1950.

Akwai dakunan kwana 775 a fadar ta Buckingham da wuraren wanka 78 da kuma kofofi har 1,514.

A duk lokacin da take gari sarauniyar Ingila na ganawa kowane mako da Firaiministan Burtaniya kuma a duk shekara tana karbar bakuncin baki fiye da 50,000 dake zuwa fadar ziyara ko kuma liyafar cin abinci.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A shekarar 2011, an gayyaci shugaban Amurka Barrack da matarsa Michelle Obama liyafar cin abinci