Kotu ta daure shugaban 'yan jarida a Masar

Yehia Qallash na cikin 'yan jaridar da suka buga labaran zanga-zangar

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Yehia Qallash na cikin 'yan jaridar da suka buga labaran zanga-zangar

An yanke wa shugaban kungiyar 'yan jaridar Masar da wasu abokan aikisa biyu hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari saboda laifin "mara gaya ga masu tayar da kayar baya."

Wata kotu a birnin Alkahira ce ta yanke hukuncin, kodayake ta amince Yehia Qallash da Gamal Abdel Rahim da kuma Khaled al-Balshy su biya $630 a bayar da su beli kafin su daukaka kara.

A watan Mayu ne 'yan sanda suka kai samame hedikwatar 'yan jaridar, inda suka kama 'yan jarida biyu.

'Yan jaridar sun buya a hedikwatar ne inda suke neman mafaka daga kamun da za a yi musu.

Ana zargin su da tunzura mutanen da suka yi wa gwanatin kasar bore saboda mika tsiburai biyu na Tekun Bahar Maliya ga Saudiyya.

Masu sukar Shugaba Abdul Fattah al-Sisi sun yi tur da mika tsiburan suna masu cewa yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

An tsare wasu Misrawa da 'yan jaridar kasashen waje na dan wani lokaci a farkon wannan shekarar yayin da suke halartar zanga-zangar da aka yi kan kyamar mika tsiburan.