Paparoma ya nada manyan limaman Cocin Roman Katolika 17

Kadinal Dieudonne Nzapalainga, Archibishop na Banguia Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na cikin sababbin limaman

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kadinal Dieudonne Nzapalainga, Archibishop na Banguia Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na cikin sababbin limaman

Paparoma Francis ya nada sababbin manyan limaman Cocin Roman Katolika 17 daga sassa daban-daban na duniya, kuma da dama daga cikin su ne za su zabi wanda zai gaje shi.

An zabi manyan limaman ne daga nahiya biyar, cikinsu har da wanda zai zama jakadan fadar Vatican a kasar Syria.

Wakilin BBC a Rome David Willey ya ce wadannan sababbin nade-nade sun sha bamban da yadda aka saba.

Limaman dai sun kai kashi uku cikin hudu na limaman da za su zabi mutumin da zai gaje shi.

Dokar Vatican ta ce limaman da ke kasa da shekara 80 ne kawai za su iya zaben wanda zai gaji Paparoman.

Limamai 13 cikin wadanda aka nada a ranar Asabar na da shekaru kasa da 80, don haka sun cancanci su gaje shi.

Wannan shi ne karo na uku cikin shekara uku da Paparoma ya nada sababbin limaman Cocin.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Archibishop na Kuala Lumpur, Anthony Soter Fernandez, lokacn da ake taya shi murnan zaman babban limamin Katolika

Sababbin limaman

Mario Zenari, daga Italiya (zai ci gaba da zama jakada a Syria)

Dieudonne Nzapalainga, daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Carlos Osoro Sierra, daga Spain

Sergio da Rocha, daga Brazil

Blase J Cupich, daga Amurka USA

Patrick D'Rozario, daga Bangladesh

Baltazar Enrique Porras Cardozo, daga Venezuela

Jozef De Kesel, daga Belgium

Maurice Piat, daga Mauritius

Kevin Joseph Farrell, daga Amurka

Carlos Aguiar Retes, daga Mexico

John Ribat, daga Papua New Guinea

Joseph William Tobin, daga Amurka

Anthony Soter Fernandez, daga Malaysia

Renato Corti, daga Italiya

Sebastian Koto Khoarai,daga Lesotho

Ernest Simoni, daga Albania