BH: Al'ummar Maiduguri na cikin fargaba

Sojojin Najeriya na ci gaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram a yankunan jihar Borno

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya na ci gaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram a yankunan jihar Borno

A Najeriya, yanzu haka jama'a da dama a Maiduguri babban birnin jihar Borno na ci gaba da fargabar hare-haren kunar bakin wake daga 'yan kungiyar Boko Haram.

A 'yan kwanakin nan dai an yi ta fuskantar hare hare akai-akai a cikin birnin da ma wasu kauyuka da ke kusa.

Matsalar hare haren kunar bakin waken dai wani babban kalubale ne da ya dade yana ci wa jami'an tsaro a Najeriyar tuwo a kwarya.

Sai dai a nasu bangaren jami'an tsaron kasar na cewa suna iyakacin kokarin su na ganin sun kakkabe mayakan Boko Haram din.