OPEC: An kusa cimma yarjejeniyar hako mai

Helkwatar kungiyar OPEC da ke birnin Geneva

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Helkwatar kungiyar OPEC da ke birnin Geneva

Kasar Iran ta ce tana da kwarin gwiwar cewa za a cimma yarjejeniya domin rage adadin yawan man da kasashen masu arzikin mai na duniya ke hakowa.

A karshen watan nan ne kasashen da ke cikin kungiyar masu arzikin mai ta OPEC za su yi taro a Vienna domin tabbatar da kwarya-kwaryar yarjejeniyar da suka cimma ta rage yawan man da suke hakowa domin farfado da farashinsa a kasuwannin duniya.

Da ya ke ganawa da Babban Sakataren kungiyar ta OPEC, Muhammad Barkindo, Ministan mai na kasar Iran, Bijan Zanganeh, ya ce akwai kwarin gwiwa matuka na cewa ministocin harkokin makamashi na kasashen OPEC za su amince da yarjejeniyar da aka cimma a kasar Algeriya a watan Satumba.

Ya kara da cewa, takwarorinsu na fadi-tashi domin ganin an cimma wannan buri, kuma bayanan da Dr Barkindo ya yi masa na karfafa gwiwa ne.

Shi dai Muhammad Barkindo na ziyara a birnin Tehran ne a ci gaba da rangadin da yake yi domin ganin an cimma matsaya kan batun man da kasashe mabobin kungiyar ke hakowa, da nufin farfado da farashinsa wanda ya fadi warwas a kasuwannin duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babban Sakataren kungiyar ta OPEC, Muhammad Barkindo

Wani kamfanin dillancin labarai na Iran, ya ambato Mistan Barkindo yana cewa ya samu tabbaci daga hukumomin kasar cewa Iran za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an amince da wannan shiri.

Ana sa rana za a fitar da cikakken bayani kan yarjejeniyar da za a sanyawa hannu a babban taron da kungiyar za ta yi a Vienna a ranar 30 ga watan nan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Rahotanni sun bayyana cewa OPEC na hasashen samun farashin da bai gaza dala 55 zuwa 65 ba kan kowacce gangar mai daya.

A karkashin sabuwar yarjejeniyar, Iran da Libya da Najeriya za su samu damar ci gaba da hako man kamar yadda suke yi a yanzu saboda matsalolin da suke fama da su iri daban daban.

Iran ta samu wannan dama ce saboda shekarun da ta shafe tana cikin takunkumin tattalin arziki, abinda ya sa man da take fitarwa ya ragu matuka.

Yayin da Najeriya kuma ke fama da hare-haren masu tayar da kayar baya a yankin Naija Delta, ita kuwa Libya, yakin basasar da ta fada ne ya kusan durkusar da fannin man kasar baki dayansa.

Kasashen da dama da tattalin arzikinsu ya dogara a kan mai ciki har da Najeriya, sun shiga cikin matsin tattalin raziki saboda raguwar kudaden shiga da kuma faduwar darajar takardun kudaden su.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin sabanin siyasa tsakanin kasar Saudiyya da Iran, da kuma yunkurin shawo kan sauran kasashe masu arzikin mai wadanda ba sa cikin kungiyar ta OPEC, ka iya kawo cikas ga wannan yunkuri.