Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tsaya takara karo na huɗu

Angela Merkel ta zama Shugabar Gwamnatin Jamus a shekarar 2005

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Angela Merkel ta zama Shugabar Gwamnatin Jamus a shekarar 2005

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na hudu, in ji wasu mambobin jam'iyyarta ta CDU.

Ana sa ran Mrs Merkel, mai shekara 62, za ta bayar da sanarwar tsayawa takararta ranar Lahadi a hedikwatar jam'iyyarta ta the Christian Democratic Union (CDU).

Za a gudanar da babban zaben kasar ne a shekara mai zuwa.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar kan mulkin Mrs Merkel ta nuna cewa farin jinin Shugabar ya ragu, amma har yanzu ana son ta.

Jam'iyyarta ta sha kaye a zaben yanki da aka yi a farkon wannan shekarar kuma jam'iyyar AfD mai ra'ayin mazan-jiya na kalubalantarta.

Bayan zaben ne Mrs Merkel ta ce ita ce da alhakin kayen da suka sha a jihohi da dama.

Ta amince cewa shirye-shiryenta na na yin sassauci kan bakin-haure su ne suka sanya wasu 'yan kasar suka tsane ta.

Mrs Merkel ta fara shugabancin Jamus ne a shekarar 2005.

Idan ta lashen shekara mai zuwa za ta kafa tarihi irin na Helmut Kohl, wanda ya shugabancin kasar bayan yaki.

Dokokin Jamus ba su iyakance adadin wa'adin da shugaban kasa zai yi yana mulki ba.