Fadan da ke amfani da maganin sauro a matsayin magani

Mista Lethebo Rabalago da mutanen Cocinshi
Bayanan hoto,

Majami'u da dama a Afirka ta Kudu na amfani da tsafe-tsafe wajen warkar da mutane

An yi Allah-wadai da wani malamin coci a Afirka ta Kudu wanda yake fesa wa mutanen cocinshi maganin sauro domin yi musu magani.

A wani sako da aka wallafa a shafin Facebook, malamin cocin, Lethebo Rabalago, ya yi hasashen cewa wani maganin sauro wanda ake kira Doom yana iya warkar da mutane masu fama da cututtuka.

Kamfanin da ke samar da maganin sauro na Doom ya yi gargadi a kan fesa maganin.

Yayin da wani kwamishina na gwamnatin kasar ya bukaci duk wanda abin ya shafa ya aike da korafinsa.

Amma Malamin cocin ya kare kanshi, inda ya shaida wa BBC cewa yana amfani da maganin domin sama wa mutane lafiya.

Kasar Afirka ta Kudu dai ta sha samun aukuwar ire-iren hakan inda ake amfanin da tsafe-tsafe wajen warkar da mutane.

A wasu hotuna da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta, Mista Rabalago, wanda shugaba ne a cocin Mountzion General Assembly da ke lardin Limpopo, an gano shi yana fesa maganin sauron a idanu da kuma wasu sassan jikin mutanen cocin.

Ya shaida wa wakiliyar BBC Nomsa Maseko cewa ya fesa maganin a fuskar daya daga cikin matan cocin saboda tana da matsala a idanunta.

Ya kara da cewa "ba abinda zai samu matar saboda ta yi imani da Allah".

Ya kara da cewa maganin sauron zai iya warkar da cutar daji da kuma ta HIV.