Trump: Amurka za ta fice daga yarjejeniyar TPP

Masu zanga-zanga a Washington

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Da ma Amurkawa sun yi zanga-zangar rashin amince da yarjejeniyar

Shugaban Amurka mai-jiran-gado, Donald Trump, ya ce kasar za ta fice daga yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakaninta da kasashen yankin Fasifik a ranakkun farko na mulkinsa.

Kasashe 12 ne dai suka kulla wannan yarjejeniyar, wadanda idan aka hada su wuri daya sune ke rike da kashi 40% na tattalin arzikin duniya.

Mr. Trump - dan jam'iyyar Republican - ya kuma yi alkawarin rage tsauraran ka'idojin da '' ke yin karan tsaye wajen samar da ayyuka'' a fannin hakar kwal.

Sai dai bai ce komai ba game da maye gurbin tsarin inshorar lafiya na Obamacare da wani tsarin ko gina katanga kan iyakar Amurka da Mexico, kamar yadda ya ce zai yi a lokacin yakin neman zabensa.

A ranar Litinin, Farayi Ministan Japan Shinzo Abe ya ce yarjejeniyar TPP za ta kasance marar ma'ana idan babu Amurka a ciki.