Masar: Kotu ta yi watsi da hukuncin daurin rai-da-rai kan Morsi

Masar Mohammed Morsi

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mohammed Morsi na fuskantar zarge-zarge da dama

Babbar kotun daukaka kara ta kasar Masar ta sauya hukuncin daurin rai-da-rai da aka yanke wa hambararren Shugaban kasar Mohammed Morsi.

Kotun ta bada umarnin a sake yi wa Morsi, mai shekaru 65, shari'a kan tuhumar da ake yi masa na hada kai da kungiyoyin kasashen waje.

A makon jiya ne kotun ta yi watsi da hukuncin kisa da aka yanke wa Morsi a wata shari'a ta da ban kan zargin fasa gidan yari a lokacin tarzomar shekara ta 2011.

Amma har yanzu yana fuskantar dauri na tsawon lokaci a gidan yari kan wasu tuhume-tuhume biyu.

Morsi shi ne zababben shugaban kasar na farko a shekara ta 2012, amma sojoji suka tumbuke shi bayan shekara guda, bayan wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa.

Tun a wannan lokacin ne mahukunta suka kaddamar da farmaki kan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Morsi, abin da ya haddasa arangama tsakaninsu da jami'an tsaro, tare da garkame dubbanni a gidan yari.

A cikin watan Mayun 2015 ne aka yanke wa Morsi da sauran shugabannin kungiyar uku hukuncin daurin rai-da-rai bisa zargin hada kai da wasu kungiyoyin kasashen waje wurin haddasa fitina a kasar.

Kana an kuma yankewa wasu mutum 16 hukuncin kisa a shari'ar.

Masu gabatar da kara sun yi zargi kungiyar da yunkurin aikewa da wasu sakonni zuwa sansanonin kungiyar Palasdinawa ta Hamas da Hezbolla ta kasar Labanon, da kuma dakarun Revolutionary Guards na Iran.

Amma kuma kungiyar ta Brotherhood ta musanta wadannan zarge-zarge.