Turkiyya ta janye dokar yin afuwa ga mazan da suka yi fyade

Turkiyya birnin Ankara

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An yi ta gudanar da zanga-zanga a birnin Ankara kan dokar

Firai Ministan Turkiyya Binali Yildirim ya janye kudirin dokar da za ta bari a yi afuwa ga mazan da aka yankewa hukunci kan yiwa kananan yara fyade idan suka amince su aure su.

Mista Yildirim ya ce an mayar da kudirin dokar ne don bayar da isasshen lokacin sake dogon nazari, daga bangaren jam'iyyun adawa da za su fitar da na su bukatun.

Dokar dai wani yunkuri ne na yin garanbawul ga tsarin shari'a, wacce aka sake mayarwa don kara yin nazari, sa'oi kadan kafin kada kuri'a a majalisa.

Batun dai ya haddasa gagarumar zanga-zanga a fadin kasar, sannan kasashen waje sun yi ta Allah-wadai da ita.

Masu suka sun ce wannan doka za ta halasta fyade da kuma karfafa auren wuri ga yara mata.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga gwamnati da kada ta amince da kudirin dokar, da cewa za ta haifar da koma baya a yunkurin da kasar ke yi na shawo kan matsalar lalata da kananan yara da auren wuri.

Amma kuma gwamnatin ta ce dokar na da nufin yin afuwa ne ga mazajen da aka daure kan auren, kuma za ta shafi yaran da suka cewa da yardar su ne ko ta iyayensu.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan adawa a Turkiyya na cewa dokar koma baya ce ga Firam Minista Yildirim

Daga shekara 18 ne dokar Turkiyyar ta amince a aurar da yarinya, amma kuma al'adar aurar da kananan yara da shekarunsu suka gaza ta zaman ruwan dare a kasar.

Masu suka dai sun ce kasa kamar Turkiyya wacce maza ne suka fi mamaye harkoki, karamar yarinya ba za ta iya bayyana abin da ke ran ta ba, don haka kudirin dokar zai halarta yin fyade da kuma auren wuri.

Kananan yara 'yan kasa da shekara 18 su 440,000 ne suka haihu tun daga shekara ta 2001, yayin da 15,937 daga cikinsu ke kasa da shekara 15.

Cin zarafin kananan yara a kasar Turkiyya ya ninka har sau uku a cikin shekara goma, a lokacin da aka aurar da kananan yara da ba su kosa ba kimanin 438,000.