An garzaya da mawakin Amurka Kanye asibitin birnin Los Angeles

Kanye West
Bayanan hoto,

West ya katse rangadin da yake yi a Sacramento cikin karshen mako

An garzawa da Kanye West mawakin nan mai salon wakar Rap na Amurka zuwa asibiti a birnin Los Angeles.

Wani mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a birnin na LA ya shaidawa BBC cewa a ranar Litinin ne suka samu kiran waya na gaggawa , amma ba a fadi sunan mawakin ba.

Ya ce daga bisani aka sake kiran wayar kan batun rashin lafiyar mawakin, kana ofishin hukumar kwana-kwana ya amsa kiran.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwanan a birnin Los Angeles ya ce an garzaya da mutumin da ba a bayyana sunansa ba zuwa asibiti don bincikar lafiyarsa.

Ya ce " Da misalin karfe 13:20 ne agogon yankin Pacific, hukumar ta dau mataki kan bukatun taimakon gaggawar rashin lafiyar da ba a bayyana irin ta ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Babu martani daga West ko wakiliansa game da lamarin

Akwai rahotanni daga kafafen yada labarai daban-daban masu cin karo da juna game da bayanai da ke danganta batun da sunan West.

Kafar yada labarai ta NBC ta ce daukar mataki kan kiran wayar agajin rashin lafiya da kuma matakin kwantar da West a asibiti don saboda kariya da kula da lafiyarsa ne.

Kafar yada labarai ta TMZ ma kwarmata bayanai ta yi a shafin yanar gizo inda ta ce, an garzaya da West zuwa asibiti don gudanar da bincike kan abinda ya shafi ''kwakwalwa da damuwa'' , kuma ana yi masa magani kan ''rashin samun isasshen barci''.

Ita kuma jaridar Los Angeles Times ta bada rahoton cewa akwai kiran wayar neman agajin gaggawa ta layin 911 daga adireshin dake nuna ofishin kwana-kwana.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu fitattun mawaka na aikewa West sakonnin karfafa guiwa a shafukan sada zumunta

Babu dai wani martani daga West ko kuma wasu wakilansa kan bayanan da hukuma ta bayar game da lamarin.

An dai katse rangadin da mawakin West ke kan yi sakamakon faruwar wannan lamari a cikin karshen mako.

Kafin fitar wadannan labarai na jinyar West a asibiti, surukar West, Kris Jenner ta shaida wa wasu kafafan yada labarai na Amurka dalilan da suka saka aka katse rangadin na sa.

"Ya galabaita, a gajiye yake. Ya yi rangadi mai cike da wahalhalu, don haka yana bukatar ya huta".

Wasu fitattun mawaka sun rika mika sakon nuna damuwa da fatan alkahiri ga West, suna mai karfafa masa gwiwa a shafukan sada zumunta.