Nigeria ta kulla yarjejeniyar gina hanyar kankare da Dangote

Najeriya Dangote

Asalin hoton, Dangote

Bayanan hoto,

Gwmnatin Najeriya sun yi yarjejeniya da Dangote kan ginin hanya

Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejenniya da kamfanin Dangote domin gina hanyar kankare mai nisan kilomita 42 daga garin Obajana zuwa Kabba a jihar Kogi.

A yammacin ranar Talata ne bangarorin biyu suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja.

Babban sakatare a ma'aikatar ayyuka da gidaje da wutar lantarki Injiniya Magaji Abdullahi Gusau ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin tarayyar.

Yayin da mai bai wa shugaban kamfanin na Dangote shawara Injiniya Joseph Makoju ya sa hannu a madadin kamfanin, yana mai cewa "babban cigaba ne a tarihin Najeriya".

Kamfanin na Dangote zai kashe kimanin Naira biliyan 11 da rabi a aikin, amma an ba shi aikin ne a madadin biyan kudin haraji na sama da Naira biliyan biyar.

Kamfanin ya ce watanni 24 ne lokacin da aka amince kare kwangilar, amma ya ce ya kudiri aniyar kammala wa a cikin watanni 16.