Nigeria: Da kyar wasu jama'a ke samun na cin abinci

Nigeria: Da kyar wasu jama'a ke samun na cin abinci

Wasu magidanta a Najeriya suna ji a jika sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma koma bayan tattalin arziki a kasar.

Daga dukkan alamu wannan hali zai kara tsananta bayan da hukumar kididdiga ta kasar ta ce an samu karin koma-bayan tattalin arziki da kashi 2.2 cikin dari a watanni ukun da suka gabata.

An danganta wannan matsala da rashin isassun kudaden kasashen waje da kuma hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

A kan haka ne wakilinmu a Kano Mukhtar Adamu Bawa ya ziyarci wani magidanci a gidansa don ganin yadda suke cin abincin dare.