Yadda ake rayuwa a birnin Mosul da ke hannun IS

Sama da mako biyar ana ta fafatawa a yawancin birnin Mosul wanda ke hannun kungiyar IS, inda dakarun Iraki ke son ganin sun kwato birnin.

Jama'a da dama na zaune a garin inda gwamnati ta bukaci da su ci gaba da zama, saboda a kauce wa kwararar 'yan gudun hijira.

To ko a wanne hali suke zaune a birnin wanda ake wa lugudan wuta.