Kotu ta daure 'Hyena' shekara biyu a gidan yari

Iyayen 'yan matan da shugabanin al'umomi ke biyan Mista Eric kudi dan ya sadu da 'ya'yan na su
Babbar kotun kasar Malawi, ta daure mutumin da ya shaida wa BBC ya sadu da mata 104 alhali yana dauke da cutar HIV ko Sida, shekara biyu a gidan yari da horo mai tsanani.
Kotun ta samu Eric Aniva da laifin aikata mummunar al'ada, da tilasta wa amare da matan da mazajensu suka rasu yin jima'i.
A cikin watan Yuni Aniva ya yi hira da BBC, inda ya bayyana yadda yake lalata da amare da matan da mazajen su suka rasu, dalilin da ya sa shugaban kasar Peter Mutharika ya sa aka kama shi.
Tun farko an so a tuhumi Aniva da laifin lalata kananan yara, amma babu yarinyar da ta amince ta bayar da shaidar hakan.
Saboda haka aka tuhume shi da laifin aikata mummunar al'ada karkashin dokar Malawi ta biyar kan dai-daiton jinsi, mai dauke da bayanan lalata da matan da mazajensu suka mutu.
An samu mata biyu wadan da mazajensu suka mutu, inda suka bayar da shaidar cewa ya yi lalata da su.
Lawyan Aniva, Michael Goba Chipeta, ya ce zai daukaka kara kan tuhuma da hukuncin da aka yanke.