Mutum hudu sun mutu a rikicin Bamendan Kamaru

Mutane hudu ne suka mutu a Bameda da ke Kamaru

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Tun a ranar Talata fada ya barke a Bameda

Lauyoyi da malamai na adawa kan tilasta musu yin amfani da Faransanci a yankin da ake magana da harshen Faransanci da Turanci a garin Bamenda da ke Kamaru.

Shugaban jam'iyar adawa ta Social Democratic Front, John Fru Ndi wanda aka haifa a Kudu maso Arewacin kasar, ya ce mutum hudu ne suka mutu a yayin zanga-zangar.

Fada ya barke ne bayan da kungiyar malamai ta Kamaru ta yi kiran zanga-zanga kan yadda harshen Faransanci ya mamaye harkar koyarwa a makarantu fiye da harshen Ingilishi.

Rashin jituwa ya barke tsakanin masu amfani da harshen Ingilishi da na Faransa a wasu sassan kasar, inda lauyoyi suka bukaci a fassara dokokin kasar zuwa harshen Ingilishi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

John Fru Ndi ya dade yana kiraye-kiraye da a bai wa masu yin harshen Ingila karin damar cin gashin kai

Jami'an tsaro sun yi harbi da alburushi da jefa barkonon tsohuwa ga masu yin zanga-zanga, wadanda suka zargi gwamnati da hade yankin da ake amfani da harshen Ingilishi. Yawancin Kamaru na amfani da harshen Faransanci ne.

Shaidu sun kwatanta yadda ake dukan mutane, da harbinsu da kafa da jan su a kasa da sojoji suka dinga yi.

Tun a ranar Litinin masu zanga-zanga suka dauki akwatin gawa da korayen ganye suka dunga yawa a kan tituna suna bukatar da aka kara samar da damarmaki ga masu yin harshen Ingilishi