Bukola Saraki: Ban aikata laifin komai ba

Bukola Saraki: Ban aikata laifin komai ba

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya shaida wa BBC cewa bai san adadin dukiyar da ya mallaka ba, amma ya samu kashi 95% na dukiyar ne kafin ya shiga siyasa.

Sai dai bayanan da kotun kula da da'ar ma'aikata ta fitar sun nuna cewa ya mallaki dimbin dukiya da kadarori a ciki da wajen kasar.

Mista Saraki na fuskantar shari'a kan zargin yin karya a kadarorin da ya bayyana kafin ya zama gwamnan jihar Kwara a shekarar 2003, lamarin da ya musanta.

Ya shaida wa Naziru Mikailu cewa akwai cin hanci a Najeriya, amma ya ce ya tara dukiyarsa ne saboda ludufin da Allah ya yi wa iyayensa da kuma kwazonsa.