An kama masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Chadi

An damke masu shirya zanga-zanga a Chadi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Idriss Deby ya hau kujerar mulki a Chadi a 1990

Jami'an tsaro sun kama mambobi 11 na bangaren adawa a Chadi, kafin a tuhume su da laifin shirya wata zanga-zangar kyamar gwamnatin kasar.

Tun a ranar 17 ga watan Nowanba ne suka so gudanar da zanga-zangar, amma hukumomi suka haramta gudanar da ita.

Dukkan wadanda ake tsare da su 'yan bangaren adawa ne masu neman sauyi da ake kira Fonac, masu yin gangami kan tsarin da gwamnati ke bi na kawar da fatara a Chadi.

Lauyen kungiyar ta FONAC, Alain Kagombe, ya shaida wa BBC cewa an kama mambobin ne a lokacin da jami'an tsaro suka kutsa kai wurin da 'yan adawar ke gudanar da wani taro.

Shugaba Idriss Deby ya hau kujerar mulki a Chadi a 1990, bayan juyin mulkin da ya yi wa Hissene Habre.

Ya sake yin nasara a karo na biyar a zaben watan Aprilun 2016, zaben da 'yan adawa suka ce an tabka magudi.