Mata 100: Yadda Hafsat Abdulwaheed ta kalubalanci gwamna

Hajiya Hafsat Abdulwaheed ce mace ta farko da aka wallafa littafinta na kagaggen labari da harshen Hausa.

A shirinmu na "Mata 100: Muryar Rabin Al'ummar Duniya", marubuciyar ta yi bayani a kan rayuwarta ta rubutu, da ma yadda ta kalubalanci wani gwamnan jiha a Najeria da nufin tika shi da kasa a zabe.