Wani mutum ya mutu bayan an yi gasar cin abinci a Japan

Onigiri

Asalin hoton, Thinkstock

Wani dan kasar Japan ya mutu kwana uku bayan ya ƙware sakamakon gasar cin shinkafa da sauri-sauri da aka yi.

Mutumin, wanda ba a fadi sunasa ba, ya suma a wurin gasar da ke Hikone ranar 13 ga watan Nuwamba bayan ya yi yunƙurin cinye shinkafar da aka cika kwano biyar da ita a cikin minti uku.

Mutanen da suka sanya gasar sun shaida wa gidajen watsa labarai na Japan cewa mutumin ya mutu ne a asibiti kwana uku bayan aukuwar lamarin.

Gasar cin abinci da sauri-sauri ta yi fice a kasar ta Japan, inda ake tara masu kallo.

Masana sun yi gargadin cewa gasar kan jawo shaƙewa, kana wadanda suke yin ta na kasadar iya fada da ciwon ciki da na uwar-hanji.