Lufthansa ya soke tashin jirgi 900

Tambarin Lufthansa da kuma jadawalin jiragen da aka soke tashin su.

Asalin hoton, AP

Kamfanin jiragen saman Lufthansa ya soke tashin jirgi 900 bayan kotu ta bai wa matuka jirgin damar shiga yajin-aiki.

An fara yajin-aiki na kwana biyu ne da tsakar daren Talata a agogon kasar, kuma Lufthansa ya ce fasinja 100,000 lamarin zai shafa.

Kamfanin ya ce yajin-aikin ba zai shafi jiragensa da ke wasu kasashen ba irin su Eurowings, Swiss, Austrian Airlines, da Brussels Airlines.

Yajin-aikin dai wani bangare ne na kokarin da ma'aikatan kamfanin suka shafe tsawon lokaci suna yi a kan karin albashin.

Kungiyar tana so a kara wa matukan jirage su 5,400 kashi 3.7 na albashin da ake ba su tun daga shekarar 2012.

Kungiyar matuka jiragen sama, Vereinigung Cockpit, ya shiga yajin aiki sau 14 tun daga watan Aprilun shekarar 2014.

Sau biyu Lufthansa yana yunkurin hana yajin-aikin a gaban kotu ranar Talata.

Sai dai kotun da ke birnin Frankfurt ta yi watsi da bukatar kamfanin.