Nigeria: An saki mutum 40 da aka sace a Zamfara

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sace-sace sun zama ruwan dare a Najeriya

Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce an saki mutum sama da 40 da masu fashin shanu suka sace a farkon a makon jiya.

Barayin da suka sace mutanen dai sun sha alwashin ba za su sake su ba sai gwamnatin jihar ta sakar musu shanun da suka ce ta karbe musu.

Akasarin mutanen da aka yi awon gaba da su dai 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa daga kauyukansu.

Sai dai kakakin gwamnan jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya shaida wa BBC cewa an saki mutanen bayan wata yarjejeniya da suka cimma da wadanda suka sace su.

Amma ya ki yin bayani a kan ko an biya wa barayin bukatun da suka zayyana.

Rahotannin sun kara da cewa 'yan sanda biyu da farar hula hudu sun rasa rayukansu sakamakon ba-ta-kashi a lokacin da barayin suka sace mutanen.

Jihar ta Zamfara dai na fama da matsalolin rashin tsaro sakamakon yawaita hare-haren barayin shanu.