An samu maganin ƙara ƙarfin mazakuta a ofishin shugabar Korea ta Kudu

An kasar sun kwashe kwana da kwanaki suna zanga-zanga domin ganin Ms Park ta sauka daga mulki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kasar sun kwashe kwana da kwanaki suna zanga-zanga domin ganin Ms Park ta sauka daga mulki

Zargin badakalar cin hanci da ake yi wa shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye ya dauki sabon salo bayan da aka gano magungunan da ke kara karfin mazakuta a ofisoshinta.

Hukumomi sun gano magungunan ne a lokacin da suke bincike kan cinhanci a ofisoshin Ms Park.

Gwamnati ta ce an sayo magungunan ne domin bai wa marasa lafiya.

Ana zargin shugabar kasar da kyale kawarta, Choi Soon-sil, ta tsoma baki a harkokin gudanar da kasar.

Ofishin shugaban kasar ya tabbatar da cewa an sayo magungunan kara karfin mazakuta 364 da wasu magungunan irin sa da zummar yin maganin sha'awa ga jami'an da za su je Gabashin Afirka, kodayake ba a taba yin amfani da su ba.

Wakilin BBC a birnin Seoul, Stephen Evans ya ce samun magungunan kara karfin mazan zai sa 'yan kasar su ci gaba da kyamar shugabar.

'Yan kasar ta Korea ta Kudu da dama dai suna yi wa Shugaba Park kallo a matsayin wacce take rayuwa "a wata duniya ta daban" lamarin da ya sa suke matsa mata lamba ta sauka daga mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maganin kara karfin mazakuta