An gano birnin da ya shekara 5,000 a Masar

Picture shows what has been described as a grave in a city unearthed in southern Egypt that has been described as more than 5,000 years old.

Asalin hoton, MA'AIKATAR KULA DA KAYAN TARIHI TA MASAR

Masu binciken kayan tarihi na karkashin kasa a Masar sun gano wani birni wanda ya fi shekara 5,000 da wasu gine-gine, ciki har da gidaje da tukwane da manyan kaburbura.

An gano birnin ne a lardin Sohag da ke kudancin kasar ta Masar, yankin da birnin Luxor, daya daga cikin wuraren da masu ziyarar bude ido suka fi zuwa, yake.

Masana sun ce girman kaburra 15 da aka gano ya nuna cewa mutanen da aka binne a cikinsu masu-fada-a-ji ne na wancan zamanin.

Asalin hoton, MA'AIKATAR KULA DA KAYAN TARIHI TA MASAR

Asalin hoton, MA'AIKATAR KULA DA KAYAN TARIHI TA MASAR

An yi amannar cewa mutanen da suka zauna a birnin manyan jami'ai ne da kuma magina kaburbura, wadanda watakila suka gina kaburran manyan sarakuna a birnin Abydos - inda aka gina wuraren bauta da dama, kuma babban birni na farkon tarihin daular Masar ta wancan lokacin.

Farfesa Chris Eyre, masanin tarihin kasar Masar da ke Jami'ar Liverpool, ya shaida wa BBC cewa: "Akwai wata babbar makabartar da ake binne sarakunan waccan daular kusan mil daya daga wurin da aka gano wannan birni. Hasalima mun fara samun sunayen sarakunan da aka binne a makabartar. Don haka ina ganin wannan gari shi ne birnin farko a tarihin Masar."

An gano wanna birni ne a lokacin da hukumomin kasar ke kokarin farfado da fannin bude ido na kasar, wanda ya fuskanci koma-baya sakamakon hatsaniyar siyasar da aka rika yi a shekarun baya bayan nan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A farkon wannan watan ne masu bincike daga Spain suka gano wata gawa da aka alkinta ta hanyar sanya mata sinadarai a kusa da Luxor

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wuraren tarihi da ke kusa da Luxor suna jan hankalin masu yawon bude ido